Freedom Radio

Shugaba Buhari zai shirya liyafar cin abinci ga wasu Shugabannin duniya


Yanzu haka dai ana gudanar da faretin girmamawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a dandalin Eagles square da ke birnin tarayya Abuja, a wani bangare na gudanar da taron bikin ranar dimokradiyya.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda suka halarci taron akwai sabon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan da takwaran sa na wakilai Femi Gbaja-bia-mila sai kuma wasu daga cikin manyan shugabanni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara zagaye sojojin da suke je fareti a matsayin mafarin bude taro, wanda ke gudana yanzu haka a filin wasa na Eagles square.

Daga cikin shugabannin da suka halarci taron akwai na kasashen Rwanda, Sierra Leone, Ghana, Namibia, Niger, Congo, Liberia, Gambia da kuma Guinea Bisau.

Sauran sun hadar da mataimakan shugabannin kasashen Sudan, Uganda ta kudu da na Zimbabwe, da kuma Masar, sai wakilan Jamhuriyar Benin, Equatorial Guinea, Gabon, Jamhuriyar Cek, Faransa, Ireland, Japan, Mali, Kenya, Morroco, Malawi da kuma Belgium.

A cewar rahotanni mukaddashin babban jojin Najeriya da shugabar ma’aikata ta tarayya da kuma babban sufeton ‘yan sandan kasar nan hadi da sauran shugabannin hukumomin tsaro ne suka halarci taron.

Sauran sun hadar da jagoran jam’iyyar APC na kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin Kano da Kogi, Yobe, Kwara, Kebbi, Ekiti, Kaduna da kuma Anambra.Source link

Related posts

Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga

Naija Digest

Hukumar EFCC ta ce zata yi aiki da hukumar NYSC wajen dakile ayyukan batagari

Naija Digest

Kotun daukaka kara ta soke karar da Onnoghen ya shigar gabanta –

Naija Digest