Freedom Radio

Kotun daukaka kara: Sanata Ademola ya cancanci tsayawa takara a zaben da ya gabata


Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ce dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke ya cancanci tsayawa takara a yayin zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a shekarar da ta gabata.

Kotun mai kunshe da alkalai uku ta amince da daukaka karar da Sanata Ademola Adeleke da kuma jam’iyyar sa ta PDP su ka yi.

Da ya ke karanta sakamakon hukuncin mai shari’a Emmanuel Agim ya kuma ce kotun ta bukaci wadanda suka shigar da kara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja wato wahab Raheem da Adam habib da su biya Sanata Adeleke tarar naira miliyan 3.Source link

Related posts

UNICEF:Kimanin dalibai miliyan 8 ne basa zuwa makaranta a jihohin Najeriya 10

Nigerian Digest

Lagos:kudan zuma sun kashe wani jami’in hukumar yaki da fasakwauri –

Nigerian Digest

Aisha Bahari ta soki shirrin Gwamnatin tarayya na rage fatara –

Nigerian Digest