Freedom Radio

Hukumar NYSC ta gargadi Hukumomin Jami’o’in Najeriya –


Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta kasa NYSC, ta gardadi hukumomin jami’o’in kasar nan da su guji tura dalibai zuwa bautar kasa, da suka saba ka’idojin ta.

Daraktan Janar na Hukumar Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana haka, a wani taron karawa juna sani a birnin tarayya Abuja, da ya gudana a daren jiya.

Birgediya ya kuma ce, hukumar NYSC ba zata saurara kowanne Jami’a ba, idan har ta gano suna tura dalibai zuwa bautar kasa bayan munzalin su bai kai su gudanar da hidimar kasar ba.

Ya kuam ce, hukumar a yanzu haka na shiryawa daliban jami’o’in kasar nan rukunin ’’B’’ shiga sansanonin horaswa a wayan Yunin mai kamawa, inda kuma za a ci gaba da biyan su Naira dubu Talatin a kowanne wata.

Source link

Related posts

WHO:zata waiwaye cutar dake alaka da tabin hankali

Nigerian Digest

EFCC na bincikar Rochas Okorocha da wasu Kusoshin Gwamnati –

Nigerian Digest

Borno:kimanin mutane 30 ne suka mutu a wani hari da aka kai yankin Konduga

Nigerian Digest