Freedom Radio

Dorayi-Giza:Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wasu iyalai su uku


Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wasu iyalan gida su  uku a yankin  Dorayi-Giza a cikin karamar hukumar Kumbotso da daren jiya Laraba.

Wutar dai ta tashi ne da misalin karfe 11 na dare amma kuma kafin a shawo kanta sai tayi sanadiyar mutuwar mutanen.

Ana dai zargin cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki d aka kawo da karfin gaske, daga bisanin kuwa sai suka ji wani kara.

Daya  daga cikin  makwabcin sa  da wakilin mu ya gana da shi ya bayyana cewar suna tare da maigidan kafin daga bisani ya tashi daga wajen hirarn yana mai yi musu bankwana da cewar baci yake ji.

A cewar shakikun marigayin da shigar sa ne sai gobarar ta tashi wanda yayi sanadiyar mutuwar mai dakin sa da shi maigidan da kuma ‘yar su guda.

Amma kuma da wakilin mu Abba Isa Muhammadu ya tuntubi kakakin kamfanin samar da wuta shiyyar Kano Sani Shawai kan zargin da al’umar yankin Dorayi-Giza suka yi kan wuta mai karfi da aka kawo ya musanta zargin, yayin da ya bukaci al’ummar yankin da su dinga neman kwararru da za su hada musu wuta.

Yayin da kuma hukumar kashe gobara ta jihar nan ta ce mata da masaniya kan tashin gobarar a yankin karamar ta Kumboto.

Mai Magana da yawun hukumar Sa’adu Muhammad Ibrahim ya ce kawo yanzu babu wanda ya kai musu rahoton kan mumunan labarin sai dai yayi kira ga al’umma da su dinga gaggauta kai rahoton gobara don daukar mataki na gaba.Source link

Related posts

Kotu ta ba da umarni rufe asusun da ake zargin na tsohon gwamnan jihar Lagos

Naija Digest

NLC:sunyi barazanar tsunduma yajin aikin gama gari

Naija Digest

Katsina:wani jirgin shalkwabta rundanar sojin kasar nan yayi hadari

Naija Digest