Freedom Radio

CP na Jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya zama sabon CP na Kano –


Babban sefeton ‘yan sanda na Najeriya Muhammadu Adamu ya daba umarnin da a gagauta maida kwamishinan ‘yan sanda Ahmad Iliyasu zuwa jihar Kano a matsayin sabon kwamishinan “yan sanda na jihar Kano bayan da wa’adin aiki na CP Wakili Mohammed ya kare.

A rana 26 ga watan da muke ciki ne wa’adi aikin kwaminan ‘yan sanda Wakili Mohammed ya kare bayan ya kai shekaru 35 yana aiki.

Sabon kwamishinan ‘yan sandan na jihar Kano Ahmed Iliyasu na rike da digiri na 2 kan harkokin kasuwanci daga jam I’ar Ambrose Ali dake Ekpoma kafin daga bisani a maida shi shalkwata rundunar ‘yan sanda dake Abuja, a matsayin babban jami’I.

Haka zalika a shekara ta 2016 zuwa watan Junairun wannan shekarar ya rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ogun.

Source link

Related posts

Kotu ta bukaci hukumar hana fasakwauri biyan diyar naira biliyan 90

Naija Digest

Yemi Osinbajo ya bayyana Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo abun koyi

Naija Digest

Daurawa ya ajiye mukaminsa na shugaban Hisba –

Naija Digest